Hausa
Sorah Al-Waqi'ah ( The Event )
Verses Number 96
Idan mai aukuwa ta auku.
Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.
Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.
Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
Kuma kun kasance nau'i uku.
Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?
Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,
Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
A ckin Aljannar ni'ima.
Jama'a ne daga mutãnen farko.
Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu.
Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.
Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.
Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.
Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.
Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.
Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.
Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.
Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.
A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.
Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.
Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
(Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.
Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya.
Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.
Da wani ruwa mai gudãna.
Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.
Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.
Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.
Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.
Sa'an nan Muka sanya su budurwai.
Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.
Ga mazõwa dãma.
Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.
Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.
Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?
Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.
Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.
Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.
Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.
Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.
Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"
"Shin, kuma da ubanninmu na farko?"
Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."
"Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."
"Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"
"Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."
"Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."
"Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."
"Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."
Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.
Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?
Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?
Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?
Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba,
A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.
Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?
Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?
Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?
Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.
(Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"
"Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"
Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?
Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?
Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?
Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?
Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?
Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.
Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.
To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.
Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.
Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
A cikin wani littafi tsararre.
Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.
Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.
To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.
Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
Da ƙõnuwa da Jahĩm,
Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci.