Hausa
Sorah Al-Infitar ( The Cleaving )
Verses Number 19
Idan sama ta tsãge.
Kuma idan taurãri suka wãtse.
Kuma idan tẽkuna aka facce su.
Kuma idan kaburbura aka tõne su.
Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.
Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
Mãsu daraja, marubũta.
Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.
Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.
Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.
Bã zã su faku daga gare ta ba.
Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?
Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?
Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.